M. Sh 11:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku kiyaye faɗarsa, da dokokinsa da farillansa, da umarnansa kullum.

2. Yau fa ku sani ba da 'ya'yanku nake magana ba, waɗanda ba su sani ba, ba su kuma ga hukuncin Ubangiji Allahnku ba, da girmansa, da ƙarfin ikon dantsensa,

3. da alamunsa, da ayyukan da ya yi a kan Fir'auna Sarkin Masar, da dukan ƙasar,

4. da irin abin da ya yi wa sojojin Masar, da dawakansu, da karusansu, da yadda ya sa ruwan Bahar Maliya ya haɗiye su, a sa'ad da suke bin sawunku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf,

5. da abin da ya yi muku a jeji kafin ku iso wannan wuri,

6. da abin da ya yi wa Datan, da Abiram, 'ya'yan Eliyab, ɗan Ra'ubainu, yadda ƙasa ta buɗe a tsakiyar Isra'ilawa ta haɗiye su da dukan 'ya'yansu, da alfarwansu, da dukan abu mai rai wanda yake tare da su.

7. Amma idanunku sun ga manyan ayyukan nan da Ubangiji ya aikata.”

8. “Don haka fa, sai ku kiyaye dukan umarnan da na umarce ku da su yau domin ku sami ƙarfin da za ku haye, ku shiga, ku ci ƙasar da za ku mallaka,

9. domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku da zuriyarsu, ƙasar da yake da yalwar abinci.

M. Sh 11