1. Sai shugabannin gidajen iyalan 'ya'yan Gileyad, ɗan Makir, jikan Manassa, ɗan Yusufu, suka zo suka yi magana da Musa da sauran shugabanni.
2. Suka ce, “Ubangiji ya umarce ka ka raba wa Isra'ilawa gādon ƙasar ta hanyar jefa kuri'a. Ubangiji kuwa ya umarce ka ka ba 'ya'ya mata na Zelofehad, ɗan'uwanmu, gādo.
3. Amma idan suka auri waɗansu daga waɗansu kabilan jama'ar Isra'ila, wato za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura, wato ka ga an ɗebe daga cikin namu gādo ke nan.
4. Sa'ad da shekara ta hamsin ta murnar Isra'ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, da haka za a ɗebe gādonsu daga gādon kabilar kakanninmu.”