L. Kid 33:37-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Da suka kama hanya daga Kadesh suka sauka a Dutsen Hor a kan iyakar ƙasar Edom.

38. Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba'in ta fitowar jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar.

39. Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku sa'ad da ya rasu a Dutsen Hor.

40. Sai Sarkin Arad, Bakan'ane wanda yake zaune a Negeb, a ƙasar Kan'ana, ya ji zuwan Isra'ilawa.

41. Isra'ilawa kuma suka tashi daga Dutsen Hor, suka sauka a Zalmona.

42. Daga Zalamona suka sauka a Funon.

43. Da suka tashi daga Funon, sai suka sauka a Obot.

44. Suka kuma kama hanya daga Obot suka sauka a Abarim a karkarar Mowab.

45. Suka tashi daga nan suka sauka a Dibon-gad.

46. Suka tashi daga Dibon-gad suka sauka a Almon-diblatayim.

47. Da suka tashi daga Almon-diblatayim, suka sauka a duwatsun Abarim a gaban Nebo.

48. Daga duwatsun Abarim suka sauka a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.

49. Suka sauka kusa da Urdun, suka kakkafa alfarwansu tun daga Betyeshimot har zuwa Abel-shittim, a filayen Mowab.

50. Sai Ubangiji ya yi magana da Musa a filayen Mowab kusa da Urdun, daura da Yariko, ya ce

51. ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan'ana,

52. sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu.

53. Sa'an nan ku mallaki ƙasar, ku zauna a ciki,gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.

54. Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.

55. Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi.

56. Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su.”

L. Kid 33