13. Sai Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar Isra'ila suka fita zango su tarye su.
14. Musa kuwa ya husata da shugabannin sojoji waɗanda suke shugabannin dubu dubu da shugabannin ɗari ɗari, waɗanda suka dawo daga wurin yaƙi.
15. Ya tambaye su ya ce, “Don me kuka bar dukan mata da rai?
16. Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal'amu, suka yaudari Isra'ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama'ar Ubangiji.
17. Yanzu, sai ku kashe dukan yara maza da kowace mace wadda ta san namiji.
18. Amma dukan 'yan mata da ba su san maza ba, sai ku bar wa kanku.
19. A cikinku duk wanda ya kashe mutum ko ya taɓa gawa, sai ya zauna a bayan zango kwana bakwai don ya tsarkake kansa tare da bayin a rana ta uku da ta bakwai.
20. Za ku tsarkake kowace riga, da kowane abu da aka yi da fata, da kowane kaya da aka yi da gashin awaki, da kowane abu da aka yi da itace.”
21. Ele'azara firist kuwa, ya ce wa sojojin da suka tafi yaƙi, “Waɗannan su ne ka'idodin da Ubangiji ya ba Musa.
22. Zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma,
23. da dukan abin da wuta ba ta ci ba, su ne za ku tsarkake su da wutar tsarkakewa, duk da haka za a kuma tsarkake shi da ruwa. Amma abin da wuta takan ci, sai a tsarkake shi da ruwa kawai.