4. Da Musa ya ji wannan, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu'a.
5. Sa'an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade.
6. Kai, Kora da ƙungiyarka duka, gobe, sai ku ɗauki farantan ƙona turare.
7. Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”
8. Musa ya ci gaba da magana da Kora. “Ku Lawiyawa ku kasa kunne!
9. Kuna ganin wannan ƙaramar magana ce, wato cewa Allah na Isra'ila ya keɓe ku daga cikin jama'ar Isra'ila domin ya kawo ku kusa da shi, ku yi aiki a alfarwar sujada ta Ubangiji, ku kuma tsaya a gaban jama'a don ku yi musu aiki?
10. Ya yarda ka zo kusa da shi, kai da dukan 'yan'uwanka Lawiyawa, a yanzu kuwa sai ƙoƙari kuke ku karɓi aikin firist!
11. Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!”
12. Musa kuwa ya aika a kirawo Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!
13. Kana jin ƙaramin abu ne da ka fitar da mu daga cikin ƙasar mai yalwar abinci, don ka kashe mu a jeji? So kake kuma ka mai da kanka sarki a bisanmu?
14. Banda wannan kuma, ga shi, ba ka kai mu zuwa cikin ƙasa mai yalwar abinci ba, ba ka ba mu gonaki da gonakin inabi domin mu gāda ba, yanzu kuwa kana so ka ruɗe mu, to, ba za mu zo ba sam!”
15. Musa kuwa ya husata ƙawarai da gaske, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace ko jakinsu ba, ban kuwa cuce su ba.”
16. Musa ya ce wa Kora, “Kai da ƙungiyarka duka ku hallara a gaban Ubangiji gobe, da kai, da su, da Haruna.
17. Sa'an nan kowane ɗayanku ya ɗauki farantinsa na ƙona turare, ya zuba turaren wuta a ciki, ya kawo a gaban Ubangiji, wato farantan ƙona turare guda ɗari biyu da hamsin ke nan. Kai kuma da Haruna kowannenku ya kawo nasa faranti.”
18. Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa'an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna.