L. Kid 16:29-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Idan mutanen nan sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, idan abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba.

30. Amma idan Ubangiji ya aikata wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara zuwa cikin lahira a raye, sa'an nan za ku sani mutanen nan sun raina Ubangiji.”

31. Musa ya rufe bakinsa ke nan, sai wurin da Datan da Abiram suke tsaye, ƙasar ta dāre

32. ta haɗiye su tare da iyalansu, da dukan mutanen Kora, da dukan mallakarsu.

33. Haka fa, su da dukan abin da yake nasu suka gangara zuwa lahira da rai.

34. Sai Isra'ilawa duka waɗanda suke kewaye da su suka gudu saboda kururuwansu, suka ce. “Mu mā gudu,kada kuma ƙasa ta haɗiye mu.”

35. Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.

36. Ubangiji ya ce wa Musa,

37. “Ka faɗa wa Ele'azara, ɗan Haruna firist, ya kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, ka watsar da gawayin daga farantan a wani wuri gama farantan tsarkakakku ne.

38. Waɗannan farantan ƙona turaren sun zama tsarkakakku sa'ad da aka miƙa su a bagaden Ubangiji. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo, musu mutuwa, ka ƙera murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, ta haka za su zama gargaɗi ga jama'ar Isra'ila.”

L. Kid 16