L. Kid 16:1-2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1-2. Sai Kora, ɗan Izhara, na kabilar Lawi, iyalin Kohat, ya yi ƙarfin hali ya tayar wa Musa. Waɗansu uku kuma daga kabilar Ra'ubainu suka haɗa kai da shi, su ne Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, da On,ɗan Felet, da waɗansu Isra'ilawa su ɗari biyu da hamsin, sanannun shugabanni da jama'a suka zaɓa.

3. Suka taru a gaban Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun cika izgili, gama dukan taron jama'a na Ubangiji ne, Ubangiji kuwa yana tare da su. Me ya sa kai Musa ka aza kanka shugaba a kan taron jama'ar Ubangiji?”

4. Da Musa ya ji wannan, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu'a.

5. Sa'an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade.

6. Kai, Kora da ƙungiyarka duka, gobe, sai ku ɗauki farantan ƙona turare.

7. Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”

L. Kid 16