Sai Kora, ɗan Izhara, na kabilar Lawi, iyalin Kohat, ya yi ƙarfin hali ya tayar wa Musa. Waɗansu uku kuma daga kabilar Ra'ubainu suka haɗa kai da shi, su ne Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, da On,ɗan Felet, da waɗansu Isra'ilawa su ɗari biyu da hamsin, sanannun shugabanni da jama'a suka zaɓa.