4. Tattarmukan da suke cikinsu kuwa suka faye kwaɗayin nama, har Isra'ilawa ma da kansu suka fara gunaguni suna cewa, “Wa zai ba mu nama mu ci?
5. Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, da su kakamba, wato wani irin kayan lambu ne mai yaɗuwa, da guna, da sāfa, da albasa, da tafarnuwa.
6. Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.”
7. Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne.
8. Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.
9. Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.
10. Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko'ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.
11. Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?