L. Fir 26:36-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. “Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za su kuwa fāɗi.

37. Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake ba wanda yake korarsu. Ba za su sami ikon tsaya wa maƙiyansu ba.

38. Za ku mutu a cikin al'ummai. Ƙasar maƙiyanku za ta haɗiye ku.

39. Sauranku da kuka ragu za ku lalace a ƙasashen maƙiyanku saboda muguntarku da ta kakanninku, za ku lalace kamarsu.

40. “Amma za su hurta muguntarsu da ta kakanninsu, da cin amana da suka yi mini, da kuma tayarwa da suka yi mini,

41. haka kuma ni na tayar musu, na kai su ƙasar maƙiyansu. Amma idan sun ƙasƙantar da kangararriyar zuciyarsu, suka tuba, suka bar muguntarsu,

42. sa'an nan zan tuna da alkawarina wanda na yi wa Yakubu, da Ishaku, da Ibrahim, zan kuwa tuna da ƙasar.

43. Amma za su fita daga ƙasar, ƙasar kuwa za ta ji daɗin hutunta muddin ba su ciki, tana zaman kango. Amma za su tuba saboda sun ƙi kula da ka'idodina, suka yi watsi da dokokina.

44. Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.

L. Fir 26