Josh 8:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai Joshuwa ya sallame su, suka tafi inda za su yi kwanto. Suka yi fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma shi ya kwana tare da jama'a.

10. Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe ya tattara mutanen, ya tafi tare da shugabannin Isra'ilawa, suka wuce gaba, suka bi da mutane zuwa Ai.

11. Dukan mayaƙan da suke tare da shi, suka tafi kusa da birnin, suka kafa sansaninsu arewacin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari.

12. Ya kuma zaɓi mutum wajen dubu biyar (5,000) ya sa su yi kwanto tsakanin Betel da Ai, yamma da birnin.

13. Mutanensu suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na 'yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Joshuwa ya kwana a kwarin.

14. A sa'ad da Sarkin Ai ya ga wannan, shi da mutanensa duka, wato mutanen birnin, suka gaggauta, suka tafi da sassafe zuwa gangaren wajen Araba don su gabza yaƙi da Isra'ilawa, amma bai san akwai 'yan kwanto a bayan birnin ba.

15. Sai Joshuwa da mutanensa duka suka nuna kamar an rinjaye su, suka yi ta gudu, suka nufi jeji.

Josh 8