11. Da jama'a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama'ar.
12. Mutanen Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da 'yan'uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su.
13. Mutum wajen dubu arba'in ne (40,000), mayaƙa, suka haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa filayen Yariko.
14. A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra'ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa.
15. Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa,
16. “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun.”
17. Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun.
18. Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.