1. Da al'umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,
2. “Ɗauki mutum goma sha biyu daga cikin jama'a, wato mutum ɗaya na kowace kabila.
3. Ka umarce su su ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, su haye da su, su ajiye su a masaukin da za su kwana yau.”
4. Sai Joshuwa ya kirawo mutum goma sha biyu waɗanda ya zaɓa daga cikin Isra'ilawa, mutum guda na kowace kabila.
5. Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra'ila.
6. Wannan zai zama alama a gare ku, don ya yiwu wata rana 'ya'yanku za su tambaye ku, su ce, ‘Ina ma'anar waɗannan duwatsu a gare ku?’
7. Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.”