Josh 14:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne karkasuwar gādon da Isra'ilawa suka karɓa a ƙasar Kan'ana, wanda Ele'azara, firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin iyalan kabilan Isra'ila suka ba su.

2. Kabilan nan tara da rabi sun karɓi nasu rabon gādo ta hanyar jefa kuri'a, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

3. Gama Musa ya riga ya ba kabilan nan biyu da rabi nasu gādo a wancan hayin Kogin Urdun wajen gabas, amma bai ba Lawiyawa rabon gādo ba.

4. Jama'ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu.

5. Jama'ar Isra'ila fa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, suka rarraba ƙasar ta hanyar kuri'a.

6. Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa'an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina.

Josh 14