1. Sa'ad da Yabin Sarkin Hazor ya ji labari, ya aika wa Yobab, Sarkin Madon, da Sarkin Shimron, da Sarkin Akshaf,
2. da sarakunan da suke arewacin ƙasar tuddai, da cikin Araba a kudancin Kinneret, da cikin filayen kwari, da cikin Dor a yamma.
3. Ya kuma aika zuwa ga Kan'aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa.
4. Sai suka fita tare da dukan mayaƙansu, babbar runduna mai yawa kamar yashi a bakin teku, da dawakai, da karusai da yawa ƙwarai.
5. Da sarakunan nan duka suka haɗa ƙarfinsu, sai suka je suka kafa sansaninsu a wuri ɗaya a bakin ruwayen Merom domin su yi yaƙi da Isra'ilawa.
6. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, gama gobe war haka zan ba da su ga Isra'ilawa, su karkashe su duka. Za ku daddatse agaran dawakansu, ku kuma ƙone karusansu.”
7. Sai Joshuwa, tare da dukan mayaƙansa, suka je suka mame su, suka auka musu a bakin ruwayen Merom.