Josh 10:21-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sa'an nan dukan mutane suka koma wurin Joshuwa a sansani a Makkeda lafiya. Ba kuma mutumin da ya tsokani Isra'ilawa.

22. Sa'an nan Joshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon, ku kawo mini waɗannan sarakuna biyar da suke a kogon.”

23. Suka yi haka nan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon.

24. Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.

25. Sai Joshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, gama haka Ubangiji zai yi da dukan abokan gābanku waɗanda za ku yi yaƙi da su.”

26. Sa'an nan Joshuwa ya buga su, ya kashe su, ya kuma rataye kowane ɗayansu a bisa itace. Suka yini a rataye har maraice.

27. Amma sa'ad da rana take faɗuwa, Joshuwa ya umarta, aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan, aka jefa su cikin kogon inda suka ɓuya. Sa'an nan suka rufe bakin kogon da manyan duwatsu. Har wa yau suna nan.

28. A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.

29. Joshuwa ya zarce, da shi da dukan Isra'ilawa zuwa Libna, suka yi yaƙi da Libna.

Josh 10