Ish 8:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al'umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro!

10. Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.

11. Bisa ga ikonsa mai girma Ubangiji ya faɗakar da ni kada in bi hanyar da jama'ar ke bi. Ya ce,

12. “Kada ka haɗa kanka da jama'a cikin ƙulle-ƙullensu, kada kuma ka ji tsoron abubuwan da su suke jin tsoro.

13. Ka tuna fa, ni Ubangiji Mai Runduna, mai tsarki ne. Wajibi ne ni kaɗai za ka ji tsoro.

14. Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama'ar mulkokin Yahuza da Isra'ila da mutanen Urushalima.

15. Da yawa za su yi tuntuɓe su faɗi. Za su faɗi, a kuwa ragargaza su. Za a kama su da tarko.”

16. Almajiraina su ne za su lura, su kuma kiyaye jawabin da Allah ya ba ni.

17. Ubangiji ya ɓoye kansa daga jama'arsa, amma ni na dogara gare shi, na kafa zuciyata a gare shi.

18. Ga ni tare da 'ya'yan da Ubangiji ya ba ni. Ubangiji Mai Runduna, wanda kursiyinsa a kan Dutsen Sihiyona yake, ya maishe mu rayayyen jawabi ga jama'ar Isra'ila.

Ish 8