8. Ubangiji ya ce,“Ina ƙaunar aikin gaskiya,Amma ina ƙin zalunci da aikata laifi.Da aminci zan ba mutanena lada,In yi madawwamin alkawari, da su.
9. Za su yi suna a cikin al'ummai,Dukan wanda ya gan su zai sani,Su ne mutanen da na sa wa albarka.”
10. Urushalima tana murna saboda abin da Ubangiji ya yi.Tana kama da amaryar da ta sha ado a ranar aurenta.Allah ya suturce ta da ceto da nasara.