Ish 60:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa.Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi.Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!

7. Dukan tumaki na Kedar da Nebayot,Za a kawo miki su hadaya,A kuwa miƙa su a kan bagade domin Ubangiji ya ji daɗi.Ubangiji zai darajanta Haikalinsa fiye da dā.

8. Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai,Kamar kurciyoyi suna komowa gida.

9. Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe,Suna kawo mutanen Allah gida.Suna tafe da azurfa da zinariya,Domin su girmama sunan Ubangiji,Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Wanda ya sa dukan al'ummai su girmama mutanensa.

10. Ubangiji ya ce wa Urushalima,“Baƙi ne za su sāke gina garukanki,Sarakunansu kuma za su bauta miki.Na hukunta ki da fushina,Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.

11. Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana,Domin sarakunan al'ummai su kawo miki dukiyarsu.

12. Amma al'umman da ba su bauta miki ba,Za a hallakar da su.

13. “Itatuwan fir da irinsuMafi kyau daga jejin Lebanon,Za a kawo su domin a sāke gina ki, ke Urushalima,Domin a ƙawata Haikalina,A darajanta birnina.

14. 'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo,Su rusuna, su nuna bangirma.Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki.Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’

15. “Ba za a ƙara ƙinki, a yashe ki ba,Ki zama birnin da aka fita aka bari ba kowa ciki.Zan sa ki zama babba, mai ƙayatarwa kuma,Wurin yin farin ciki har abada abadin.

Ish 60