Ish 55:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Duk mai jin ƙishi ya zo,Ga ruwa a nan!Ku da ba ku da kuɗi ku zo,Ku sayi hatsi ku ci!Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara,Ba za ku biya kome ba!

2. Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba?Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa?Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa,Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.

3. “Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni,Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai!Zan yi tabbataccen alkawari da ku,Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.

Ish 55