Ish 43:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Isra'ila, Ubangiji wanda ya halicce ku ya ce,“Kada ku ji tsoro, na fanshe ku.Na kira ku da sunanku, ku nawa ne.

2. Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi,Zan kasance tare da ku,Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba.Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba,Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.

3. Gama ni ne Ubangiji Allahnku,Allah Mai Tsarki na Isra'ila, wanda ya cece ku.Zan ba da Masar, da Habasha, da SebaGa Sairus domin fansarku.

4. Zan ba da dukan al'ummai don in ceci ranku,Gama kuna da daraja a gare ni,Gama na ba ku girma, ina kuma ƙaunarku.

5. Kada ku ji tsoro, ina tare da ku!“Daga gabas mafi nisa, da kuma yamma mafi nisa,Zan kawo jama'arku zuwa gida.

6. Zan faɗa wa kudu su bar su su tafi,Arewa kuma kada su riƙe su a can.Bari mutanena su komo daga manisantan ƙasashe,Daga kowane sashi na duniya.

7. Su mutanena ne, na kaina,Na kuwa halicce su don su girmama ni.”

8. Allah ya ce,“Kirawo mutanena a ɗakin shari'a.Suna da idanu, amma makafi ne,Suna da kunnuwa, amma kurame ne!

9. Kirawo sauran al'umma, su zo ga shari'a.A cikin allolinsu wane zai iya faɗar abin da yake a gaba?A cikinsu wa ya yi hurci a kan abin da yake faruwa yanzu?Bari waɗannan alloli su kawo shaidunsuDon su tabbatar daidai suke,Su shaida gaskiyar maganganunsu.

10. “Ya jama'ar Isra'ila, ku ne shaiduna,Na zaɓe ku al'umma, baiwata,Domin ku san ni, ku gaskata ni,Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah.In banda ni ba wani Allah,Ba a taɓa yin wani ba,Ba kuwa za a yi ba.

11. “Ni kaɗai ne Ubangiji,Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.

12. Na faɗi abin da zai faruSa'an nan na zo domin taimakonku.Ba wani gunkin da ya taɓa yin haka,Ku ne shaiduna.

Ish 43