Ish 38:12-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. An datse raina, ya ƙare,Kamar alfarwar da aka kwance,Kamar saƙar da aka yanke,Na zaci Allah zai kashe ni.

13. Dare farai na yi ta kuka saboda azaba,Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana.Na zaci Allah zai kashe ni.

14. Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi,Na kuwa yi kuka kamar kurciya,Idanuna sun gaji saboda duban sama.Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.

15. Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan.Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.

16. Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai.Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.

Ish 38