Ish 36:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa.

18. Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, da cewa Ubangiji zai kuɓutar da ku. Ko gumakan waɗansu al'ummai sun ceci ƙasashensu daga Sarkin Assuriya?

19. Ina suke yanzu, wato gumakan Hamat da na Arfad? Ina gumakan Sefarwayim? Ba ko ɗaya da ya ceci Samariya, ko ba haka ba?

20. A yaushe ko gunki ɗaya na dukan waɗannan ƙasashe ya taɓa ceton ƙasarsa daga babban sarkinmu? To, yanzu me ya sa kuke tsammani Ubangiji zai ceci Urushalima?”

21. Jama'a suka yi tsit, kamar dai yadda sarki Hezekiya ya faɗa musu, ba su amsa da kome ba.

22. Sa'an nan Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka kyakkece tufafinsu don baƙin ciki, suka tafi, suka faɗa wa sarki abin da shugaban mayaƙan Assuriya ya yi ta farfaɗa.

Ish 36