Ish 34:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Mutane za su fāɗi kamar bijiman jeji da 'yan bijimai, ƙasar za ta yi ja wur da jini, kitse kuma zai rufe ta.

8. Wannan shi ne lokacin da Ubangiji zai kuɓutar da Sihiyona, ya kuma ɗauki fansa a kan abokan gābanta.

9. Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, ƙasar za ta zama kibritu, wato farar wuta. Dukan ƙasar za ta ƙone kamar kalo.

10. Za ta yi ta ci dare da rana, hayaƙi zai yi ta tashi sama har abada. Ƙasar za ta zama marar amfani shekara da shekaru, ba wanda zai iya ƙara bi ta cikinta.

11. Mujiyoyi da hankaki su ne za su gāji ƙasar. Ubangiji zai maishe ta marar amfani, kamar yadda take tun kafin halitta.

12. Ba sarkin da zai yi mulkin ƙasar, dukan shugabanni kuma za su ƙare.

13. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro su yi girma a cikin dukan fādodi da garuruwa masu garuka, diloli da mujiyoyi za su zauna a cikinsu.

14. Namomin jeji za su yi ta kaiwa da komowa a can suna kiran juna. Mugun naman jeji zai je can ya nemi wurin hutawa.

15. Mujiyoyi za su yi sheƙarsu a can, su nasa ƙwayaye, su ƙyanƙyashe 'ya'yansu, su kuma lura da su a can. Ungulai za su tattaru a can a kai a kai.

16. Bincika cikin Littafin Ubangiji ka karanta abin da yake faɗa. Ba ko ɗaya cikin halittattun nan da zai ɓata ba, ba kuwa wanda zai rasa ɗan'uwansa. Ubangiji ne ya umarta ya zama haka, shi kansa zai kawo su tare.

17. Ubangiji ne zai rarraba musu ƙasar, ya kuma ba ko wannensu nasa rabo. Za su zauna a ƙasar shekara da shekaru, za ta kuwa zama tasu har abada.

Ish 34