6. Mazaunan kogin za su ji wari sa'ad da yake ƙafewa a hankali. Iwa da jema za su bushe.
7. Dukan amfanin gonakin da aka shuka a gaɓar Kogin Nilu za su bushe, iska ta fyauce su.
8. Duk wanda sana'arsa ta kama kifi ce a Kogin Nilu zai yi ƙugi ya yi kuka, gama ƙugiyoyinsa da tarunansa za su zama marasa amfani.
9. Waɗanda suke yin tufafin lilin za su fid da zuciya,
10. shugabanni da ma'aikata za su karai su kuma damu.
11. Shugabannin birnin Zowan wawaye ne! Mutanen Masar mafi hikima za su ba da gurguwar shawara! Ta ƙaƙa za su iya dosar sarki su faɗa masa, cewa su ne suka gāji masana da sarakuna na dā can?
12. Sarkin Masar, ina mashawartan nan naka masu hikima? Watakila za su iya faɗa maka shirye-shiryen da Ubangiji Mai Runduna ya yi domin Masar.
13. Shugabannin Zowan da na Memfis wawaye ne. Su ake zaton za su bi da al'ummar, amma sai suka bi da su a karkace.
14. Ubangiji ne ya sa su ba da gurguwar shawara. Sakamakon haka sai Masar ta yi ta aikata dukan abu a hugunce, tana tangaɗi kamar bugagge wanda santsi na kwasarsa cikin aman da ya yi.
15. A Masar duka, attajiri da matalauci, ƙarami ko babba, ba wanda zai iya yin wani taimako.
16. Lokaci zai yi in da zuciyar mutanen Masar za ta narke kamar mata. Za su yi rawar jiki da razana lokacin da suka ga Ubangiji Mai Runduna ya miƙa hannunsa don ya hukunta su.
17. Mutanen Masar za su firgita saboda Yahuza, kowane lokaci za su tuna da ƙaddarar da Ubangiji Mai Runduna ya shirya dominsu.
18. A wannan rana, za a yi amfani da harshen Ibrananci a birane biyar na Masar. Mutanen da suke can za su riƙa yin rantsuwarsu da sunan Ubangiji Mai Runduna. Za a sa wa ɗaya daga cikin biranen nan suna, “Birnin Hallaka.”