Irm 8:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Ka faɗa musu, ka ce, ni Ubangiji nace,‘Wanda ya fāɗi ba zai sāke tashi ba?Idan wani ya kauce ba zai komo kanhanya ba?

5. Me ya sa, mutanen nan naUrushalima suke ratsewa, sukekomawa baya kullayaumin?Sun riƙe ƙarya kan-kanSun ƙi komowa.

6. Na kula sosai, na saurara,Amma ba wanda ya faɗi watamaganar kirki,Ba wanda ya taɓa barin muguntarsa,Kowa cewa yake, “Me na yi?”Kamar dokin da ya kutsa kai cikinfagen fama.

7. Ko shamuwa ta sararin sama ma, tasan lokatanta,Tattabara da tsattsewa, da gaurakasuna kiyaye lokacin komowarsu.Amma mutanena ba su san dokokinaba.

8. Ƙaƙa za ku ce, “Muna da hikima,Dokar Ubangiji tana tare da mu”?Ga shi kuwa, alkalamin ƙarya namagatakarda, ya yi ƙarya.

9. Za a kunyatar da masu hikima.Za su tsorata, za a kuma tafi da su.Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji.Wace hikima suke da ita?

Irm 8