1. “Ni Ubangiji na faɗa, cewa a wancan lokaci, za a fitar da ƙasusuwa daga kaburburan sarakunan Yahuza, da na sarakansu, da na firistoci, da na annabawa, da na mazaunan Urushalima.
2. Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.
3. Sauran mutanen muguwar tsaran nan waɗanda suke a wuraren da na warwatsa su, za su fi son mutuwa fiye da rayuwa. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”