1. Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, 'yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna.
2. Sarki Zadakiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehoyakim ya yi.
3. Al'amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra'ila da Yahuza, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala.Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.