Irm 51:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Babila ta zama ƙoƙon zinariya ahannun Ubangiji,Ta sa dukan duniya ta yi maye.Ƙasashen duniya sun sha ruwaninabinta, suka haukace.

8. Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, takakkarye,Ku yi kuka dominta!Ku samo mata magani domin azabarda take sha, watakila ta warke.

9. Mun ba Babila magani, amma ba tawarke ba.Bari mu ƙyale ta, kowannenmu yakoma garinsu,Gama hukuncinta ya kai sammai, yayi tsawo har samaniya.

10. Ubangiji ya baratar da mu a fili,Bari mu tafi mu yi shelar aikinUbangiji Allahnmu a cikinSihiyona.

Irm 51