Irm 51:36-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Ubangiji ya ce,“Zan tsaya muku,Zan ɗaukar muku fansa,Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu suƙafe.

37. Babila za ta zama tarin juji, wurinzaman diloli,Abar ƙyama da abar ba'a, inda bakowa.

38. Mutanen Babila za su yi ruri kamarzakuna,Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki.

39. Sa'ad da suke cike da haɗama zan yimusu biki,In sa su sha, su yi maye, su yimurna.Za su shiga barcin da ba za su farkaba.

40. Zan kai su mayanka kamar 'yanraguna, da raguna, da bunsurai.

41. “An ci Babila,Ita wadda duniya duka take yabo ancinye ta da yaƙi,Ta zama abar ƙyama ga sauranal'umma!

42. Teku ta malalo a kan Babila,Raƙuman ruwa masu hauka sunrufe ta.

43. Garuruwanta sun zama abinƙyama,Ta zama hamada, inda ba ruwa,Ƙasar da ba mazauna,Ba kuma mutumin da zai ratsa tacikinta.

44. Zan hukunta Bel, gunkin Babila,Zan sa ya yi aman abin da yahaɗiye,Ƙasashen duniya ba za su ƙarabumbuntowa wurinsa ba.Garun Babila ya rushe!”

45. “Ku fito daga cikinta, ya jama'ata,Kowa ya tsere da ransa daga zafinfushin Ubangiji.

Irm 51