Irm 51:35-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Bari mutanen Sihiyona su ce,“Allah ya sa muguntar da mutanenBabila suka yi mana ta komakansu!”Bari kuma mutanen Urushalima suce,“Allah ya sa hakkin jininmu ya komakan Kaldiyawa!”

36. Ubangiji ya ce,“Zan tsaya muku,Zan ɗaukar muku fansa,Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu suƙafe.

37. Babila za ta zama tarin juji, wurinzaman diloli,Abar ƙyama da abar ba'a, inda bakowa.

38. Mutanen Babila za su yi ruri kamarzakuna,Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki.

39. Sa'ad da suke cike da haɗama zan yimusu biki,In sa su sha, su yi maye, su yimurna.Za su shiga barcin da ba za su farkaba.

40. Zan kai su mayanka kamar 'yanraguna, da raguna, da bunsurai.

41. “An ci Babila,Ita wadda duniya duka take yabo ancinye ta da yaƙi,Ta zama abar ƙyama ga sauranal'umma!

Irm 51