Irm 51:28-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita,Sarakunan Mediyawa, da masumulkinsu, da shugabanninsu,Da kowace ƙasar da take ƙarƙashinmulkinsu.

29. Duniya ta girgiza, tana makyarkyatasaboda azaba,Gama nufin Ubangiji na gāba daBabila ya tabbata,Nufinsa na mai da ƙasar Babilakufai, inda ba kowa.

30. Sojojin Babila sun daina yaƙi, sunazaune a cikin kagaransu.Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata,An sa wa wuraren zamanta wuta,An karya ƙyamaren ƙofofingarinta.

31. Maguji yana biye da maguji a guje,Jakada yana biye da jakada,Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewaan ci birninsa a kowane gefe.

32. An ƙwace mashigaiAn ƙone fadamu da wuta,Sojoji sun gigice.

33. Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah naIsra'ila na ce,“Mutanen Babila sun zama kamardaɓen masussukaA lokacin da ake sussuka,Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbeta zai zo.”

34. Nebukadnezzar, Sarkin Babila, yacinye Urushalima,Ya ragargaza ta,Ya maishe ta kufai,Ya haɗiye ta kamar yadda dodonruwa yakan yi,Ya cika cikinsa da kayanmarmarinta,Ya tatse ta sarai.

35. Bari mutanen Sihiyona su ce,“Allah ya sa muguntar da mutanenBabila suka yi mana ta komakansu!”Bari kuma mutanen Urushalima suce,“Allah ya sa hakkin jininmu ya komakan Kaldiyawa!”

36. Ubangiji ya ce,“Zan tsaya muku,Zan ɗaukar muku fansa,Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu suƙafe.

Irm 51