Irm 5:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ku bi titunan Urushalima ko'ina!Ku dudduba ku lura!Ku bincika kowane dandali, ku gani,Ko za ku iya samun ko mutum ɗayaMai aikata adalci, mai son gaskiya,Sai in gafarta mata.

2. Ko da yake suna cewa, ‘Na rantse daran Ubangiji,’Duk da haka rantsuwar ƙarya sukeyi.”

3. Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiyakake so ba?Ka buge su, amma ba su yi nishi ba,Ka hore su, amma sun ƙi horuwa,Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse,Sun ƙi tuba.

4. Sai na ce,“Waɗannan mutane ba su da kirki,Ba su da hankali,Ba su san hanyar Ubangiji,Ko shari'ar Allahnsu ba.

5. Zan tafi wurin manyan mutane, in yimusu magana,Gama sun san nufin Ubangiji, dashari'ar Allahnsu.”Amma dukansu sun ƙi yardaUbangiji ya mallake su,Suka ƙi yi masa biyayya.

Irm 5