17. “Ku ba Fir'auna Sarkin Masarsabon suna,‘Mai yawan surutu, wanda bai rifcizarafi ba!’
18. Ni wanda sunana Ubangiji MaiRunduna Sarki ne,Na rantse da raina, wani zai ɓullo,Kamar Tabor a cikin tsaunuka,Ko kuwa kamar Karmel a bakinteku.
19. Ya ku mazaunan Masar,Ku shirya kayanku don zuwa bauta,Gama Memfis za ta lalace, ta zamakufai,Ba mai zama a ciki.
20. “Masar kyakkyawar karsana ce,Amma bobuwa daga arewa ta aukarmata!
21. Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙane, masu yawan kitse,Sun ba da baya, sun gudu, ba sutsaya ba,Domin ranar masifarsu ta zo,Lokacin halakarsu ya yi.
22. Masar tana gudu, tana huci kamarmaciji,Gama abokan gābanta suna zuwa daƙarfi,Za su faɗo mata da gatura kamarmasu saran itatuwa.
23. Ni Ubangiji na ce, za su sarikurminta,Ko da yake ba su ƙirguwa,Gama suna da yawa kamar fara,Ba su lasaftuwa.
24. Za a kunyatar da mutanen Masar,An bashe su a hannun mutanenarewa.”
25. Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi.
26. Zan bashe su a hannun waɗanda suke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.
27. “Ya bawana Yakubu, kada ka jitsoro,Kada ka firgita, ya Isra'ila.Gama zan cece ka daga ƙasa mainisa,Zan ceci zuriyarka daga ƙasarbautarsu.Yakubu zai komo, ya yi zamansa darai kwance,Ba wanda zai razanar da shi.
28. Ni Ubangiji na ce,Kada ka ji tsoro, ya bawanaYakubu,Gama ina tare da kai.Zan hallaka dukan sauran al'ummasarai inda na kora ka.Amma ba zan hallaka ka sarai ba.Zan hukunta ka yadda ya kamata,Ba zan bar ka ba hukunci ba.”