Irm 46:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma.

2. Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.

3. Masarawa suka yi ihu, suka ce,“Ku shirya kutufani da garkuwa,Ku matso zuwa wurin yaƙi!

4. Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, kuhau!Ku tsaya a wurarenku da kwalkwalia ka!Ku wasa māsunku!Ku sa kayan yaƙi!”

5. Ubangiji ya yi tambaya ya ce,“Me nake gani?Sun tsorata, suna ja da baya,An ci sojojinsu, suna gudu,Ba su waiwayen baya, akwai tsoro akowane sashi.”

6. Masu saurin gudu ba za su tsere ba,Haka nan kuma jarumi,A arewa a gefen Kogin Yufiretis,Sun yi tuntuɓe, sun fādi.

7. Wane ne wannan mai tashi kamarKogin Nilu,Kamar kogunan da ruwansu yakeambaliya?

8. Masar tana tashi kamar Nilu,Kamar kogunan da ruwansu yakeambaliya.Masar ta ce, “Zan tashi, in rufeduniya,Zan hallaka birane da mazaunacikinsu.”

9. Ku haura, ku dawakai,Ku yi sukuwar hauka, ku karusai!Bari sojoji su fito,Mutanen Habasha da Fut masuriƙon garkuwoyi,Da mutanen Lud, waɗanda suka iyariƙon baka.

10. Wannan rana ta Ubangiji, Allah MaiRunduna ce,Ranar ɗaukar fansa ce don ya ramawa maƙiyansa.Takobi zai ci, ya ƙoshi,Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi,Gama Ubangiji Allah Mai Rundunazai hallaka maƙiyansa,A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.

11. Ku mutanen Masar, ku haura zuwaGileyadDon ku samo ganye!A banza kuke morar magunguna,Ba za ku warke ba.

Irm 46