Irm 44:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Me ya sa kuke tsokanata da ayyukan hannuwanku, kuna miƙa wa gumaka hadayu a ƙasar Masar inda kuka zo don ku zauna? Yin haka zai sa a hallaka ku, ku zama abin la'ana da zargi a cikin dukan ƙasashen duniya.

9. Ko kun manta da mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakunan Yahuza da na matansu, da naku, da na matanku, waɗanda suka aikata a ƙasar Yahuza da kan titunan Urushalima?

10. Amma har wa yau ba ku ƙasƙantar da kanku ba, ba ku ji tsorona ba, ba ku kuwa kiyaye dokokina da umarnaina ba, waɗanda na ba ku ku da kakanninku.

11. “Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan aukar muku da masifa, in hallaka mutanen Yahuza duka.

12. Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la'antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya.

13. Zan hukunta dukan waɗanda suke zaune a Masar kamar yadda na hukunta wa Urushalima da takobi, da yunwa, da annoba.

14. Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”

15. Sai dukan mazan da suka sani matansu sun miƙa wa gumaka hadayu, da dukan matan da suke tsaye a wurin, da dukan Yahudawan da suke zaune a Fatros, babban taron jama'a, suka ce wa Irmiya,

16. “Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba!

17. Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.

Irm 44