Irm 44:26-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Domin haka ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da yake zaune a ƙasar Masar. ‘Ni Ubangiji na rantse da sunana Maɗaukaki, cewa ba zan yarda kuma wani mutumin Yahuza da yake ƙasar Masar ya ambaci sunana da yin rantsuwa, cewa ya rantse da zatin Ubangiji ba.’

27. Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.

28. ‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa.

29. Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika.

30. Zan kuma ba da Fir'auna Hofra, Sarkin Masar, a hannun abokan gabansa, da waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zadakiya, Sarkin Yahuza, a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila wanda ya zama abokin gābansa, ya kuwa nemi ransa.’ ”

Irm 44