Irm 44:26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Domin haka ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da yake zaune a ƙasar Masar. ‘Ni Ubangiji na rantse da sunana Maɗaukaki, cewa ba zan yarda kuma wani mutumin Yahuza da yake ƙasar Masar ya ambaci sunana da yin rantsuwa, cewa ya rantse da zatin Ubangiji ba.’

Irm 44

Irm 44:16-30