Irm 42:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shugabannin sojoji, da Yohenan ɗan Kareya, da Yazaniya ɗan Hoshaiya, da jama'a duka, daga ƙarami zuwa babba, suka zo,

2. suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka.

3. Ka yi mana addu'a domin Ubangiji Allahnka ya nuna mana hanyar da za mu bi, da kuma abin da za mu yi.”

4. Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu'a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”

5. Sa'an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji mai gaskiya, mai aminci ya zama shaida a tsakaninmu, idan ba mu yi duk yadda Ubangiji Allahnka ya aiko ka gare mu ba.

6. Ko nagari ne ko mugu ne, za mu yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu wanda muka aike ka wurinsa, gama zai zama alheri a gare mu idan mun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu.”

7. Bayan kwana goma sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya.

8. Sai Irmiya ya kira Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi, da dukan jama'a tun daga ƙarami har zuwa babba.

9. Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda kuka aike ni da koke-kokenku wurinsa ya ce,

10. ‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku.

Irm 42