1. Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim.
2. Amma shi da barorinsa, da mutanen ƙasar, ba wanda ya kasa kunne ga maganar Ubangiji wadda ya yi musu ta bakin annabi Irmiya.
3. Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu'a ga Ubangiji Allah dominmu.”
4. A lokacin nan Irmiya yana kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a tsare shi a kurkuku ba tukuna.