Irm 35:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Amma sa'ad da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo yaƙi a ƙasar, sai muka ce, ‘Bari mu tafi Urushalima domin muna jin tsoron sojojin Kaldiyawa da Suriyawa.’ Shi ya sa muke zaune a Urushalima.”

12. Sa'an nan Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

13. “Haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa, ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima cewa, ‘Ba za ku karɓi umarnina, ku kasa kunne ga maganata ba?’

14. Umarnin da Yonadab ɗan Rekab ya yi wa 'ya'yansa, kada su sha ruwan inabi, sun kuwa kiyaye shi. Ba su taɓa shan ruwan inabi ba har wa yau, domin suna biyayya da umarnin kakansu. Ni kuwa na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne gare ni ba.

15. Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.

16. 'Ya'yan Yonadab ɗan Rekab sun kiyaye umarnin da kakansu ya yi musu. Amma jama'an nan ba su yi mini biyayya ba.

17. Domin haka, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce zan kawo wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima masifar da na ce zan kawo musu, domin na yi musu magana, ba su ji ba, na kira su, ba su amsa ba.”

18. Sai Irmiya ya ce wa Rekabawa, “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Tun da yake kun kiyaye dukan abin da Yonadab kakanku ya umarce ku,

19. saboda haka Yonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa magaji wanda zai tsaya a gabana ba.’ ”

Irm 35