1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya a shekara ta goma ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza. A lokacin kuwa Nebukadnezzar yana da shekara goma sha takwas da sarauta a Babila.
2. A lokacin nan kuwa sojojin Sarkin Babila sun kewaye Urushalima da yaƙi, annabi Irmiya kuwa yana a tsare a gidan waƙafi, a fādar Sarkin Yahuza.
3. Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.
4. Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido.