Irm 31:9-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Da kuka za su komo.Da ta'aziyya zan bishe su, in komarda su,Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukanruwa,A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda baza su yi tuntuɓe ba.Gama ni uba ne ga Isra'ila,Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”

10. “Ku ji maganar Ubangiji,Ya ku al'ummai,Ku yi shelarsa har a ƙasashen da sukenesa, na gāɓar teku.Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsaIsra'ila zai tattaro ta,Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayiyakan kiyaye garkensa.’

11. Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu.Ya fanshe shi daga hannuwanwaɗanda suka fi ƙarfinsa.

12. Za su zo su raira waƙa da ƙarfi,A bisa ƙwanƙolin Sihiyona,Za su yi annuri saboda alherinUbangiji,Saboda hatsi, da ruwan inabi, damai,Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu.Rayuwarsu za ta zama kamarlambu,Ba za su ƙara yin yaushi ba.

Irm 31