7. Na yi zaton bayan da ta aikata wannan duka, za ta komo wurina. Amma ba ta komo ba, maƙaryaciyar 'yar'uwarta, wato Yahuza, ta gani.
8. Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.
9. Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa.
10. Duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.”
11. Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba.
12. Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce,“Ki komo ya Isra'ila, marar aminci,Ni Ubangiji, na faɗa.Domin ni mai jinƙai ne,Ba zan yi fushi da ke ba.Ba zan yi fushi da ke har abada ba,Ni, Ubangiji na faɗa.