5. yana cewa, ‘Sai kowane ɗayanku ya juyo daga mugun halinsa da mugayen ayyukansa don ya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku, ku da kakanninku tun daga zamanin dā har abada.
6. Kada ku bi gumaka, ku bauta musu, ku yi musu sujada, ko ku tsokane ni da ayyukan hannuwanku, sa'an nan ba zan hore ku ba.’
7. Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.
8. “Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Tun da yake kun ƙi yin biyayya da maganata,
9. zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.
10. Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu.
11. Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al'ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba'in.
12. Sa'an nan bayan cikar shekara saba'in ɗin, zan hukunta Sarkin Babila da ƙasarsa, wato ƙasar Kaldiyawa. Zan maishe ta kango har abada, saboda zunubinsa.
13. Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abin da na faɗa gāba da ita. Dukan abin da aka rubuta a wannan littafi, wato dukan abin da Irmiya ya yi annabcinsa gāba da dukan al'umman nan.
14. Al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.’ ”
15. Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce mini, “Ka karɓi ƙoƙon ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al'umman da na aike ka gare su, su sha.
16. Za su sha, su yi tangaɗi su yi hauka saboda takobin da zan aiko a cikinsu.”