Irm 17:2-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Idan sun tuna da 'ya'yansu haka sun tuna da bagadansu da Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa masu duhuwa da kan tuddai masu tsayi.

3. Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar.

4. Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”

5. Ubangiji ya ce,“La'ananne ne mutumin da yakedogara ga mutum,Wanda jiki ne makaminsa,Wanda ya juya wa Ubangiji baya,

6. Gama yana kama da sagagi ahamada,Ba zai ga wani abu mai kyau yanazuwa ba.Zai zauna a busassun wurarenhamada,A ƙasar gishiri, inda ba kowa.

7. “Mai albarka ne mutumin da yakedogara ga Ubangiji,Wanda Ubangiji ne madogararsa.

8. Shi kamar itace ne wanda ake dasa abakin rafiWanda yake miƙa saiwoyinsa zuwacikin rafin,Ba zai ji tsoron rani ba,Kullum ganyensa kore ne,Ba zai damu a lokacin fari ba,Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.

9. “Zuciya ta fi kome rikici,Cuta gare ta matuƙa,Wa zai san kanta?

10. Ni Ubangiji nakan bincike tunani,In gwada zuciya,Domin in sāka wa kowane mutumgwargwadon al'amuransa,Da kuma gwargwadon ayyukansa.

11. “Kamar makwarwar da ta kwantakan ƙwan da ba ita ta nasa ba,Haka yake ga wanda ya sami dukiyarharam,Yana gaɓar ƙarfinsa, za ta rabu dashi,A ƙarshe zai zama wawa.”

12. Kursiyi mai daraja,Da aka sa a bisa tun daga farko,Wurin ke nan inda Haikalinmuyake.

13. Ya Ubangiji, begen Isra'ila,Duk waɗanda suka rabu da kai, za susha kunya.Waɗanda suka ba ka baya a duniyaza a rubuta suDomin sun rabu da Ubangiji,maɓuɓɓugar ruwan rai.

14. Ubangiji, ka warkar da ni, zan kuwawarke,Ka cece ni, zan kuwa cetu,Gama kai ne abin yabona.

15. Ga shi, suna ce mini,“Ina maganar Ubangiji take?Ta zo mana!”

16. Amma ni ban yi gudun zamanmakiyayi a gabanka ba,Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba,Ka kuwa sani.Abin da ya fito daga bakina kuwa,A bayyane yake gare ka.

17. Kada ka zamar mini abin razana,Kai ne mafakata cikin ranar masifa,

18. Bari waɗanda suka tsananta mini susha kunya,Amma kada ka bar ni in kunyata.Bari su tsorata,Amma kada ka bar ni in tsorata.Ka aukar musu da ranar masifa,Ka hallaka su riɓi biyu!

19. Haka Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Biliyaminu, wadda sarakunan Yahuza suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukan ƙofofin Urushalima.

Irm 17