Haka Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Biliyaminu, wadda sarakunan Yahuza suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukan ƙofofin Urushalima.