Hab 1:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ga shi, ina tā da Kaldiyawa,Al'umman nan mai zafi, mai fitina,Waɗanda suke tafiya ko'ina a duniya,Sun ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.

7. Suna da bantsoro da firgitarwa.Adalcinsu da ikonsu sun danganta ga yadda suke so.

8. “Dawakansu sun fi damisa sauri,Sun fi kyarketan maraice zafin hali,Sojojin dawakansu suna zuwa a guje.Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa,Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.

9. “Sun zo don su yi kama-karya.Ana jin tsoronsu tun ma kafin su zo.Sun tattara bayi kamar yashi.

10. Sukan yi wa sarakuna ba'a,Sukan mai da masu mulki abin wasa.Kowace kagara abin dariya ce a wurinsu,Sukan tsiba ƙasa, su hau, su cinye ta.

Hab 1