Filib 4:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Na yi farin ciki da Ubangiji ƙwarai da yake a yanzu kam, kularku gare ni ta farfaɗo, ko dā ma kuna kula da ni, dama ce ba ku samu ba.

11. Ba cewa, ina kukan rashi ba ne, domin na koyi yadda zan zauna da wadar zuci a cikin kowane irin hali da nake.

12. Na san yadda zan yi in yi zaman ƙunci, na kuma san yadda zan yi in yi zaman yalwa. A kowane irin hali duka na horu da ƙoshi da yunwa, yalwa da rashi.

13. Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.

14. Amma kuwa kun kyauta da kuka taya ni cikin ƙuntatata.

15. Ku kuma Filibiyawa, ku kanku kun sani tun da aka fara yin bishara, sa'ad da na bar ƙasar Makidoniya, ba wata ikkilisiyar da ta yi tarayya da ni wajen hidimar bayarwa da karɓa, sai dai ku kaɗai.

16. Ko sa'ad da nake Tasalonika ma, kun aiko mini da taimako ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba.

17. Ba cewa, don ina neman kyautarku ba ne, a'a, nemar muku amfani nake yi, a ƙara a kan ribarku.

18. An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.

Filib 4