20. Ba ni da wani kamarsa, wanda da sahihanci zai tsananta kula da zamanku lafiya.
21. Dukansu sha'anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba.
22. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.
23. Shi ne nake fata in aiko, da zarar na ga yadda al'amarina yake gudana.
24. Na kuma amince har ga Ubangiji, ni ma da kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.
25. Amma na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas ɗan'uwana, abokin aikina, abokin famana kuma, wanda kuka aiko ya yi mini ɗawainiya.
26. Yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya.
27. Lalle ya yi rashin lafiya, har ya yi kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayinsa, ba kuwa shi kaɗai ba, har ni ma, don kada in yi baƙin ciki a kan baƙin ciki.
28. Saboda haka na ɗokanta ƙwarai in turo shi domin ku yi farin cikin sāke ganinsa, ni kuma in rage baƙin cikina.
29. Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane,
30. domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.